Da dumi-dumi: Buhari da Gbajabiamila sun yi ganawar sirri a Aso Rock

Da dumi-dumi: Buhari da Gbajabiamila sun yi ganawar sirri a Aso Rock

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 6 ga watan Satumba yayi ganawar sirri tare da kakakin majalisar wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila.

Motar Gbajabiamila ta isa fadar Shugaban kasar da misalign karfe 11:22 na safe.

Sun fara ganawa da shugaba Buhari da misalin karfe 11:30 na safe.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ganawar nasu baya rasa nasaba da kisan da ake yiwa yan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu.

Wasu mambobin majalisar wakilai sun bukaci Gbajabiamila da ya yanke hutun yan majalisar bisa lamarin hare-hare da ake kai ma yan Najeriya a Afrika ta kudu.

Suna son majalisar dokokin kasar su bayar da goyon baya ga bangaren zartarwa wajen ganin an kare yan Najeriya dake Afri ka ta Kudu.

Shugabannin na ci gaba da ganawar a daidai lokacin tattaro wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya caccaki fadar Shugaban kasa kan tura wakilai na musamman zuwa Afrika ta Kudu

A halin da akeciki, mun ji cewa tawagar da shugaba Muhammadu Buhari ya tura kasar Afirka ta kudu ta dira birnin Johannesburg, domin ganawa da shugaban kasar, Cyril Ramaphosa.

Wakilin shugaba Buhari na musamman shine shugaban hukumar leken asirin tarayya wato NIA, Ambasada Ahmed Abubakar.

Jakadan Najeriya zuwa Afrika ta kudu da sauran jami'an ofishin jakadancin sun tarbesa ne a babban filin jirgin saman O.R Tambo. Ana sa ran zai gana da shugaban kasar Afirka ta kudu a birnin Pretoriya ranar Juma'a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel