Shehu Sani ya caccaki fadar Shugaban kasa kan tura wakilai na musamman zuwa Afrika ta Kudu

Shehu Sani ya caccaki fadar Shugaban kasa kan tura wakilai na musamman zuwa Afrika ta Kudu

- Sanata Shehu Sani ya caccaki fadar Shugaban kasa akan tura wakilai na musamman zuwa kasar Afrika ta Kudu

- A ranar Laraba, 4 ga wata Satumba ne shugaba Buhari ya aika wakilai na musamman zuwa ga gwamatin Afrika ta Kudu aka hare-haren da ake kaiwa yan Najeriya

- Tsohon dan majalisar yace kamata yayi ace gwamnatin tarayya ta tura wakilai na musamman ga iyalan wadanda aka kuntatawa maimakon tura wakilai zuwa ga gwamnatin Afrika ta Kudu

Sanata Shehu Sani ya caccaki fadar Shugaban kasa aka tura wakilai na musamman zuwa Afrika ta Kudu akan hare-haren da ake kaiwa yan Najeriya da shagunansu a kasar.

Legit.ng ta rahoto cewa Sani, wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar tarayya ta takwas, ya rubuta a shafin twitter a ranar Juma’a, 6 ga watan Satumba, cewa ba daidai bane gwamnatin tarayya ta tura wata tawaga na musamman zuwa ga gwamnatin Afrika ta Kudu.

Yace kamata yayi ace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wakilai zuwa ga iyala wadanda abu ya shafa maimaiko tura wakilai zuwa ga gwamatin Afrika ta Kudu.

“Kuskure ne gwamnatin tarayya ta tura wasu wakilai zuwa ga gwamnatin kasar Afrika ta Kudu. Wadanda aka kuntatawa ya kamata a ziyarta ba wai akasin haka ba,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta sake kama wani dan Najeriya da FBI ke nema ruwa a jallo, da wasu mutum 5 a Sokoto

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tawagar da shugaba Muhammadu Buhari ya tura kasar Afirka ta kudu ta dira birnin Johannesburg, domin ganawa da shugaban kasar, Cyril Ramaphosa.

Wakilin shugaba Buhari na musamman shine shugaban hukumar leken asirin tarayya wato NIA, Ambasada Ahmed Abubakar.

Jakadan Najeriya zuwa Afrika ta kudu da sauran jami'an ofishin jakadancin sun tarbesa ne a babban filin jirgin saman O.R Tambo.

Ana sa ran zai gana da shugaban kasar Afirka ta kudu a birnin Pretoriya ranar Juma'a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel