Abubuwa 16 da baku sani ba game da marigayi Mugabe

Abubuwa 16 da baku sani ba game da marigayi Mugabe

Robert Mugabe dai shi ne tsohon Shugaban kasar Zimbabwe daga shekarar 1980 zuwa 2017. Mugabe ya samu kimanin shekaru talatin da bakwai yana shugabantar kasar. A ranar Juma’a 6 ga watan Satumba, 2019 Allah ya amshi rayuwarsa.

Kari a kan wannan ga wadansu jerin abubuwa 21 da ya kamata ku sani game da tsohon Shugaban kasan Zimbabwe:

1. Haihuwa

An haifi Robert Gabriel Mugabe ne a ranar 21 ga watan Fabrairu, 1924 a kauyen Kutama dake kudancin kasar Zimbabwe.

KU KARANTA:Tsohon Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya rasu

2. Mahaifinsa

Sunan mahaifin Mugabe, Gabriel Matibiri sana’arsa kuwa ita ce aikin kafinta.

3. Mugabe tsohon malamin makaranta ne.

4. Sunan matarsa Sally Hayfron wadda ta haifa masa Michael Nhamodzenyika Mugabe a ranar 27 ga watan Satumba, 1963.

5. Marigayi Mugabe ya shiga gidan kurkuku a shekarar 1964 inda gwamnatin kasar ta daure shi.

6. A shekarar 1980 Mugabe ya lashe zaben shugabancin kasar Zimbabwe.

7. Mugabe ya mulki Zimbabwe na tsawon shekaru 37 tun daga shekarar 1980 zuwa 2017.

8. Mugabe ya taba saduwa da sakatariyarsa Grace Marufu, inda ta samu ciki har ta haifa masa diya biyu mace mai suna bona da namiji mai suna Robert.

9. Bayan mutuwar Hayfron a shekarar 1992, Mugabe ya auri Marufu a shekarar 1996.

10. A shekarar 1997, Grace ta haifawa Mugabe yaronsu na uku Chatunga Bellarmine.

11. A shekarar 2000 Mugabe ya fadi a wani yinkurin da yayi na yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

12. A shekarar 2008 Mugabe yazo na biyu a zaben zagaye na farko inda Tsvangirai ya janye daga takarar sakamakon farmaki da aka yita kaiwa magoya bayansa.

13. A shekarar 2009 cikin halin dar-dar gwamnatin Mugabe ta nada Tsvangirai a matsayin Firai minista tsawon shekara hudu.

14. A shekarar 2017, Mugabe ya tsige mataimakinsa Emmerson Mnangagwa domin matarsa Grace tam aye gurbinsa.

15. A watan Nuwamban 2017, rundunar sojin kasan suka tursasa masa sauka daga bisa karagar mulki.

16. A ranar 6 ga watan Satumba, 2019 Allah ya karbi rayuwar Robert Mugabe, kuma ya rasu ne ya na da shekara 95 a duniya.

https://www.vanguardngr.com/2019/09/21-things-you-may-not-know-about-late-robert-mugabe-of-zimbabwe/amp/#click=https://t.co/E9fNm30nrT

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel