Babu wanda za a mayarwa da kudinsa – Oshiomhole ga yan takarar gwamna a Kogi

Babu wanda za a mayarwa da kudinsa – Oshiomhole ga yan takarar gwamna a Kogi

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Kwamrad Adams Oshiomhole a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, ya wancakalar da yiwuwar mayar wa da yan takarar da suka fadi zaben fidda gwanin gwamnan jam'iyyar a jihar Kogi kudinsu.

Oshiomhole a lokacin da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawarsa da yan takara 16, yace jam’iyyar tana da al’adan da ya kamata a cigaba da aiwatarwa.

Ba'a tantance bakwai daga cikin yan takara 16 da suka yanki fam din tsayawa takara akan kudi naira miliyan 22.5 ba, saboda wasu dalilai.

Amma dai an tantance sauran mutane tara, ciki harda Gwamna Yahaya Bello, wanda ya lashe tikitin takarar jam'iyyar.

Oshiomhole yace: “Jam’iyyarmu tana tafiyar da ayyukanta bisa dokoki. Idan akwai al’amuran da ya kamata mu tattauna akai, al’amuran APC ne kuma bai kamata a bayyana wa manema labarai ba.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta sake kama wani dan Najeriya da FBI ke nema ruwa a jallo, da wasu mutum 5 a Sokoto

“Ba wannan bane karo na farko da muke gudanar da zabe. Muna da al’adu kuma bamu da kowace rubutacciyar bukata a gabanmu.”

Shugaban APC din ya bayyana cewa dukkan wadanda basu samu nasara ba a zaben sun bada tabbacin cewa ba za su kalubalanci sakamakon zaben ba a kotu, amman zasu yi aiki don ganin nasaran jam’iyyar a lokacin zabe.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel