EFCC ta sake kama wani dan Najeriya da FBI ke nema ruwa a jallo, da wasu mutum 5 a Sokoto

EFCC ta sake kama wani dan Najeriya da FBI ke nema ruwa a jallo, da wasu mutum 5 a Sokoto

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), reshen jihar Sokoto tare da hadin gwiwar FBI, sun yi babban kamu ta hanyar kama wani mai suna Emmanuel Adedeji Oluwatosin, wanda ke cikin jerin sunayen wadanda hukumar FBI ke nema ruwa a jallo.

Shugaban hukumar na jihar, Abdullahi Lawal, yayinda yake gurfanar da mai laifin a Sokoto, yayi bayanin cewwa a kama mai laifi e a Kaduna.

Kayayyakin da aka samo a gidansa sun hada da motoci biyu kirar, Mercedes Benz E550, Mercedes Benz C450, wayar iPhone, na’urorin lafto, modem da layukan waya.

Lawal ya kara da cewa abokan ta’asar nasa a Najeriya da kasashen waje kan tattara bayanan asusun mutane wanda dashi suka yi amfanin wajen damfararsu, su kan yi shi ta fannin kasuwanci.

Daga nan sai su mayar da abubuwan da suka damfara zuwa kudi.

Shugaban na EFCC ya kara da cewa binciken farko da aka gudanar zuwa yanzu ya bayyana cewa sama da naira biliyan 1.4 aka gano a asusun mai laifin yaayinda ya zuba jarin sama da naira biliyan 70 a wani wuri. Ana kan kokarin gano kudade.

A wani lamari makamanci haka, Lawal yace hukumar ta kama wasu masu laifi da ake nema, Muzakkir Muhammad, ta wata hukuma makamancin haka, da ked a nasaba da samun kudi ta hanyar damfara da kuma buga kudaden bogi.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: An gurfanar da wani malami akan satar babur a jihar Ekiti

Yace wani mai suna Abdullahi Ibrahim ne ya kai karar mai laifin, bayan ya damfari wani, Samaila Sani, mai harkar chanji kimanin $33,850.

Har ila yau EFCC ta gurfanar da wasu jami’an gwamnatin karamar hukumar Sokoto wanda suka damfari wasu ma’aikatan gwamati ta hayar rage masu kudade daga albashinsu tu daga 2013.

Masu laifi sune; Ishaka Abdullahi (Sakatare ilimi), Abdullahi Idris (Mataimaki sakatare ilimi), Abdullahi Dadi (Ma’aji), da kuma Idris Wamabai (Akawu).

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel