Wadanda suka kai hari kamfanonin Afirka ta Kudu za su fuskanci fushin hukuma - IGP Adamu

Wadanda suka kai hari kamfanonin Afirka ta Kudu za su fuskanci fushin hukuma - IGP Adamu

- Shugaban 'yan sandan Najeriya ya ce mutane 36 ne 'yan sanda suka kama da laifin kaiwa 'yan kasar Afirka ta kudu mazauna Najeriya farmaki

- Shugaban 'yan sandan ya ce ba za a barsu su tafi haka ba, za su fuskanci hukunci

- Najeriya kasa ce da ta ginu a kan dokoki, don haka dole ne abi doka

Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayyana cewa 'yan Najeriya 36 ne aka kama da laifin watanda da kasuwancin 'yan kasar Afirka ta Kudu da sunan maida martani.

Mohammed ya sanar da manema labarai ne a ziyarar da suka kai masa a ofishin hukumar 'yan sanda da ke Ado Ekiti a ranar Alhamis.

Adamu yace Najeriya kasa ce da aka gina da dokoki kuma duk Dan kasar da aka kama da laifin nuna banbanci ga 'yan wata kasa mazauna nan za a kamasa da laifin ta'addanci da rashin kishin kasa.

KU KARANTA: Bera ya jefa ango a mummunan hali

Ya ce kamen anyi shi ne don bin doka da kuma adalci kuma a nunawa duniya cewa 'yan Najeriya na bin doka.

Shugaban 'yan sandan ya ce, "Najeriya kasa ce da aka gina akan dokoki kuma zamu bi dokokin. Ba za mu yi yadda wasu kasashen ke yi ba. Babu wanda za mu bari ya dau doka a hannhnsa. Gwamnatin tarayya na yin abinda ya dace akan harin da ake kaiwa 'yan kasar mu a kasar Afirka ta Kudu."

"Wannan ba zai baiwa 'yan Najeriya lasisin harar kadarori ko kasuwancin 'yan Afirka ta kudu ba ko wata kasar ketare. Duk wanda yayi hakan zamu gansa a matsayin Dan ta'adda kuma mara kishin kasa. A don haka ne muka kamasu kuma zamu hukuntasu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel