'Yan Boko Haram sun kai wa tawagar Gwamna Zulum hari

'Yan Boko Haram sun kai wa tawagar Gwamna Zulum hari

- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kaiwa tawagar Gwamnan jihar Borno hari

- Maharan sun budewa jerin motocin Gwamnan wuta ne a Kunduga

- Gwamnan da kwamishinoninsa sun kubuta, inda sojoji suka budewa maharan wuta

A ranar Alhamis ne 'yan ta'addan Boko Haram suka kai hari ga jerin motocin Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Abin ya auku ne misalin karfe 9 na dare.

Kamar yadda muka samu daga majiyarmu, 'yan ta'addan sun hari motocin ne a Konduga yayin da Zulum ke dawowa daga tafiya zuwa karamar hukumar Bama.

KU KARANTA: Bera ya jefa ango a mummunan hali

Zulum ya ziyarci Bayo, Kwaya Kusar, Askira Uba da Gwoza a matsayin hanyar gane kananan hukumomin 27 na jihar da kuma duba su.

Majiyar ta ce, "Gwamnan, kwamishinoninsa da sauran ababen hawa a jerin sun wuce ba tare da wani abu ya faru dasu ba. Sai dai motar karshe ta sojoji an jefe ta da alburusai,"

"Tun da su ka fara harbinmu, jami'an suka mayar da martani."

Konduga yanki ne kusa da dajin Sambisa. 'Yan ta'addan sun dade suna kai hari yankin karkashin umarnin shugabansu, Abubakar Shekau.

An kai harin ne wata 7 bayan da aka hari tsohon gwamnan jihar Kashim Shettima, wanda Zulum ya gada, akan hanyarsa ta zuwa Gamboru Ngala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel