Wani direba ya yi garkuwa da kansa don yaudarar abokinsa

Wani direba ya yi garkuwa da kansa don yaudarar abokinsa

- Wani direba ya yi garkuwa da kansa

- Ya yaudari abokinsa har ya karbi kudin fansa N350,000

- Tuni dai abokin nasa ya maka shi kotu don karbar hakkinsa

A ranar Alhamis ne 'yan sanda suka gurfanar da wani direba mai shekaru 44, mai suna Adeoya a gaban kotun Karmo da ke Abuja, sakamakon zarginsa da akeyi da shirya garkuwa da kansa tare da yaudarar abokinsa har ya biya kudin fansa N350,000.

An zargi Adeoya da laifuka biyu da suka hada da cin amana da yaudara.

Lauyan mai kara, Ijeoma Ukagha, ya sanar da kotu cewa wani mutum mai suna Daniel, mai zama a Bwari, Abuja, ya kawo rahoton ga ofishin 'yan sanda da ke Life Camp, Abuja a ranar 27 ga watan Augusta.

KU KARANTA: Bera ya jefa ango a mummunan hali

Ukagha ya sanar da cewa a ranar 23 ga watan Augusta wajen karfe 5:30 na yamma, wanda ake kara ya kira wanda ya yi kara tare da bukatar tallafinsa.

Ya sanar da shi cewa anyi garkuwa da shi har ma da 'ya'yansa a babbar hanyar Kaduna-Abuja.

Ya roke sa da ya taimaka masa da kudin fansa har N350,000 da alkawarin zai biyasa idan an sako su.

Ukagha ya kara da cewa, yayin da 'yan sanda suka yi bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin amma duk yunkurin amsar kudin ya ci tura.

Laifin ya ci karo da sashi 312 da 322 na penal code.

Alkalin kotun, Alhaji Inuwa Maiwada, ya amince da belin Adeoya akan N50,000 da kuma tsayayye mutum.

Maiwada ya dage sauraron shari'ar zuwa wani lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel