Gwamnatin jahar Zamfara za ta gina katafaren gidan masaukin baki na biliyan 9

Gwamnatin jahar Zamfara za ta gina katafaren gidan masaukin baki na biliyan 9

Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya daura tubalin gina wani katafaren gidan masaukin baki na alfarma da zai lakume kimanin naira biliyan 9, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin jahar Zamfara za ta gina wannan Otal ne a cikin garin Gusau da hadin gwiwar wata kamfani mai zaman kanta, mai suna Finesse and Estetics Nigria Limited.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kwato dabbobi 134 daga hannun barayi, sun mika ma gwamnati

Da yake jawabi a yayin bikin kaddamar da aikin ginin Otal, Gwamna Matawalle ya bayyana cewa wannan na daga cikin alkawurran daya daukan ma jama’an jahar Zamfara a ranar da aka rantsar da shi a matsayin gwamna.

“Na yi alkawarin samar da kyakkyawar yanayi da zai janyo hankulan masu zuba hannun jari daga ciki da wajen kasar nan domin su samar da guraben ayyuka ga matasanmu, wannan aikin kadai zai samar da ayyuka 3,000, yayin da Otal din zai kasance masaukin baki ga masu zuba hannun jari idan sun shigo.

“Haka zalika jahar ta yi asarar manyan tarukan gwamnatin tarayya, da tarukan kasashen duniya daban daban saboda karancin masaukan baki irin na alfarma, amma a yanzu muna sa ran kammala aikin wannan otal mai suna 100 keys paradise cikin watanni 30, kuma kamfanin Amber Hospitality ce za ta kula da gudanarwarsa.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan ya nemi dan kwangilar dake aikin ginin daya tabbata ya yi amfani da kayayyakin da ake samu a jahar Zamfara wajen aikin ginin, sai dai kuma a inda babu kayan a jahar.

Shima da yake nasa jawabin, wakilin kamfanin Finess and Estetics, Igwu Inya ya bayyana cewa zasu tabbatar da gudanar da ingantaccen aiki cikin lokacin da aka yi yarjejeniyar kammalawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel