Kashe yan Najeriya a Afirka ta kudu: Buhari zai yi ma yan Najeriya karin bayani

Kashe yan Najeriya a Afirka ta kudu: Buhari zai yi ma yan Najeriya karin bayani

Ministan watsa labaru, Alhaji Lai Muhamma ya bayyana cewa nan bada jimawa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi ma al’ummar Najeriya cikakken jawabi game da hare haren da aka kai ma yan Najeriya a kasar Afirka ta kudu.

Rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta bayyana cewa ministan ya bayyana haka ne yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, inda ya bayyana dalilan da suka sanya gwamnatin Najeriya ta dawo da jakadanta daga kasar Afirka ta kudu.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kwato dabbobi 134 daga hannun barayi, sun mika ma gwamnati

Lai ya kara da cewa gwamnati ta yi ma jakadanta kiranye ne domin tattaunawa, sai dai ba za’a yi wannan tattaunawa ba har sai tawagar yan aiken da shugaban kasa ya aika ma shugaban kasar Afirka ta kudu ta dawo gida Najeriya.

Ministan ya cigaba da cewa bayan tawagar ta dawo gida, kuma sun tattauna ne shugaban kasa Buhari zai yi ma yan Najeriya cikakken jawabi, haka nan shirin dawo da yan Najeriya gida, shiri ne da wani kamfani ta kirkiro, kuma gwamnatin tarayya ta yi maraba da shi.

Daga karshe ministan yace baya ga janyewa daga taron tattalin arziki na duniya dake gudana a kasar Afirka ta kudu, akwai wasu hanyoyi da Najeriya za ta dauka don tabbatar da tsaron yan Najeriya a Afirka ta kudun, sa’annan ya tabbatar da babu dan Najeriya ko daya da aka kashe

Don haka ya yi kira ga yan Najeriya dasu kauce ma daukan doka a hannunsu, kuma su bi a hankali wajen amincewa da duk wani bidiyo da suka gani yana yawo a shafukan yanar gizo da sunan rikicin, saboda yace akwai bidiyon karya a cikinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel