Za'a yi shara, NNPC ta yi barazanar sallaman ma'aikata 1,050

Za'a yi shara, NNPC ta yi barazanar sallaman ma'aikata 1,050

Kamfanin arzikin man feturin Najeriya NNPC, ta yi barazanar sallaman ma'aikatan ma'ajiya mai 21 dake fadin tarayya kan rashin gaskiya, amana, cin hanci da rashawa.

A binciken New Telegraph, kowace ma'ajiyar mai na da akalla ma'aikata 50.

Dirakta Manajan kamfanin NNPC, Mele Kyari, a jiya ya tabbatar da labarin cewa akwai kulle-kulle, boye-boye da cuwa-cuwan da ma'aikatan Depot suka shahara da shi.

Ya jaddadawa manajojin ma'ajiyar da ma'aikatan cewa duk wanda aka kama da rashawa zai rasa aikinsa ba tare da bata lokaci ba.

Yayinda yake jawabi a liyafan da aka shiryawa ma'aikatan, shugaban NNPC ya yi kira da ma'aikatan cewa su kamanta gaskiya wajen ayyukansu na yau da kullum saboda saboda cimma manufan ma'aikatar.

KU KARANTA: El-Rufa'i: Gwamnatin jihar Kaduna ta fara rusau

Diraktan yada labaran hukumar, Ndu Ughamadu, yace: "(Shugaban hukumar) ya ce ba zai lamunci cuwa-cuwan da aka saba yi a baya ba, duk ma'aikacin da aka kama da rashawa zai fita da ma'akatara ba tare da bata lokaci ba."

Kyari ya jawo hankalin ma'aikatan su kai karan duk wani babban da suka gani yana ha'inci kuma idan ba'a dauki mataki ba, su kawo masa.

Hakazalika, ya ce hukumar za ta karrama duk ma'aikacin da ya gudanar da aikinsa da kyau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel