Batagarin matasa sun fara rushe wani Masallaci a jihar Delta

Batagarin matasa sun fara rushe wani Masallaci a jihar Delta

Wasu batagarin matasa sun rushe wani bangare na wani masallaci da ake gina wa a Kiagbodo, wata unguwa mai rinjayen mabiya addinin Kirista, kuma mahaifar tsohon minista, Cif Edwin Clark.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa sai da shugaban karamar hukumar Burutu ya sanar da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro sannan aka dakatar da matasan daga rushe masallacin gaba daya kuma aka samu zaman lafiya a unguwar.

Vanguard ta ce gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, ya kira shugaban karamar hukumar ranar Litinin domin ya samu cikakken bayani a kan abinda ya faru.

DUBA WANNAN: Tubabban 'yan bindiga a Katsina sun sanar da Masari su waye ke haddasa rikici a Katsina

Matasan sun fara rushe masallacin ne bayan Mallam Abubakar Korekeme, mutumin dake gina Masallacin a gidansa dake Kiagbodo ya yi burus da gargadin da suka dinga yi masa a kan basa son a gina musu Masallaci a unguwarsu.

Mallam Korekeme, wanda ya bayyana cikin fushi, ya ce matasan sun zo su rushe Masallacin ne bisa umarnin wani fitaccen mutum dan asalin unguwar.

Kazalika, ya lashi takobin cewa babu wani abu da zai firgita shi har ya fasa gina Masallacin a cikin gidansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel