El-Rufa'i: Gwamnatin jihar Kaduna ta fara rusau

El-Rufa'i: Gwamnatin jihar Kaduna ta fara rusau

- Gwamnatin Malam Nasir El-Rufa'i ta dawo shirin rusau domin raya birnin jihar

- A wannan karo, za'a rusa gidaje akalla 100 domin fadada hanyar mota

- Gwamnatin ta ce ba zata bada wani tallafi ga wadanda za'a rusawa gini ba

Hukumar raya birnin jihar Kaduna KASUPDA, ta kaddamar da atisayen rushe-rushen gine-gine a fadin jihar domin fadada hanyar mota cikin shirin raya birnin Kaduna da gwamnatin ta fara.

Diraktan bincike da bahasi na hukumar, Omega Jacob, ya bayyana hakan ga manema labarai ne ranar Alhamis, 5 ga Satumba, 2019 a jihar Kaduna.

Ya ce ana gudanar da rusau ne saboda gine-ginen zamani a jihar domin cigaban tattalin arzikin jihar.

A cewarsa, wannan rausau zai bada daman fadada hanyar mota daga Waff road zuwa shataletalen NEPA zuwa Essence zuwa titin Alkali da titin Isa Kaita.

KU KARANTA: Abdulmumini Jibrin ya samu nasara a kotun zabe

Jacob ya ce kara fadin hanyar zai shafo masu shagunan dake hanyar wadanda aka aikewa sako kafin yau na bukatar su bar shagunan saboda gyara.

"Ba zamu bada wani fansa ko kudi ga masu shaguna ba saboda ba damar ginin din-din-din aka basu ba kuma ba'a sabunta a wannan shekara ba."

"Mun zabi shaguna daban-daban kuma mun sanar da masu shagunan kamar yadda doka ya tabada. Ana bada izinin kwanaki 21."

Diraktan ya ce an baiwa akalla shaguna 100 sakon izina kuma za'a baiwa sauran domin tabbatar da cewa kowa ya samu isasshen lokacin kwashe kayansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel