Babban bankin duniya ya fasa kwai, yace Najeriya na mutuwa a hankali

Babban bankin duniya ya fasa kwai, yace Najeriya na mutuwa a hankali

Babban bankin duniya a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, ya fallasa cewa Najeriya na mutuwa a hankali sakamakon sakaci da tayi da harkar noma da kuma dogaro sosai akan danyen mai wanda aka daina damawa dashi a yanzu.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin Buhari zata tabbatar da habbaka tattalin arziki ta hanyar fitar da kayayyaki, musamman a yanzu da ta gane muhimmancin harkar noma wajen tsaron abinci, samar da ayyuka da kuma rage talauci.

Yace har yanzu ma'aikatar ce gwamnati tafi ba muhimmanci wanda ya janyo hankulan shirye-shirye da dama a karkashin manufar bunkasa fannin noma.

Babban masanin tattalin noma na babban bankin duniya, Dr Adetunji Oredipe, wanda ya bayyana hakan a Abuja yayinda yake jawabi a taron noma na Afrika wanda daya daga cikin bankunan zamani ya dauki nauyin shi, yace ya kamata sarrafa tattalin arziki zuwa fannin noma ya zamo al’ada ba wai ka’ida ba tunda tattalin arzikin ya zama abun dogaro sosai.

A cewarsa, idan da Najeriya ta riki kasuwarta a fannin manja, koko, gyada da auduga, da kasar za ta dunga samun akalla dala biliyan 10 duk shekara daga wadannan kayayyaki guda uku.

Taron ya samu halartan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya samu wakilcin karamin ministan noma da ci gaban kakkara, Mustapha Shehuri; ministar harkokin mata, Misis Paulen Talen; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Shugaban bankin Sterling Bank Plc, Abubakar Suleiman.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya bani N30.8bn domin na biya basussukan albashi – Gwamna Bello

Da yake nazari ta fuskacin fannin noman kasar, wakilin bankin duniyan yace a yanzu Najeriya na daya daga cikin kasashe mafi girma wajen shigo da abinci a duniya.

Ya yi korafi cewa duk da tarin albarkattun noma da take dashi, Najeriya wacce a baya ta kasance mai taka muhimmin rawar gani a harkar noma a duniya ta rasa matsayinta a kasashen duniya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel