Yanzu-yanzu: Abdulmumini Jibrin ya samu nasara a kotun zabe

Yanzu-yanzu: Abdulmumini Jibrin ya samu nasara a kotun zabe

Dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya samu gagarumar nasara a kotun zabe a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, 2019.

Dan majalisan ya bayyana cewa an yi masa kulle-kulle iri-iri amma daga karshe Ubangiji ya basi nasara a karshe.

Abdulmumin Jibrin ya bayyana hakan ne da daren Alhamis a shafinsa na Facebook inda yake cewa:

"A yau ne kotu tayi watsi da kara da aka shigar a kan zaben muna kujerar majalisan wakilai Kiru da Bebeji. Suna ta kulle kulle amma Allah SWT Ya fisu. Muna godiya ga jamaan mu na Kiru da Bebeji da duk mutanen da suka taimaka. Godiya ya tabbata ga Allah."

KU KARANTA: Tawagar Buhari ta musamman ta dira kasar Afirka ta kudu

Mun kawo muku rahoton cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Kano, ta jaddada dakatarwar da tayi wa Abdulmumin Jibrin, dan majalisa mai wakiltan mazabar Bebeji/Kiru a majalisar Tarayya.

Jam'iyyar reshen karamar hukumar Bebeji a baya ta dakatar da dan majalisan har na tsawon shekara daya bisa zargin daukakgudanar da ayyukan da suka saba ma jam’iyyar.

Suleiman Gwarmai, shugaban APC a Bebeji, yace hukucin dakatar da dan takaran ya zo ne, bayan kwamitin mutum bakwai da aka kafa domin bincikarsa ta bayar da shawarar yin haka bayan jam’iyyar ta karbi kara akan dan majalisan.

Jam'iyyar har ila yau ta kafa kwamiti don duba ga lamarin zargin da aka yi ma Jibrin.

Amman a ranar Laraba, Ibrahim Sarina, Sakataren jam’iyya mai mulki a jihar, yace bayan karanta rahoton da aka gabatar, kwamitin ta karfafa dakatarwan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel