Kano za ta raba gidajen sauro miliyan 8 ga al’umman jihar

Kano za ta raba gidajen sauro miliyan 8 ga al’umman jihar

Gwamnatin jihar Kano tace tana shirin raba gidajen sauro milyan takwas a karkashin shirin Gwamnatin Tarayya na kore cutar zazzabin cizon sauro.

Sakataren ma’aikatar lafiya Alhaji Bala Muhammed, yace za a rarraba gidajen sauron ne kyauta ga gidaje a watan Oktoba.

Muhammed ya bayyana haka ne a taron wayar da kan jama' a ta kafofin watsa labarai da aka gudanar a Kano akan tsarin rabon gidajen sauron.

A cewar shi, yin amfani da gidajen sauron yanda ya kamata ne hanya mafi sauki na magance zazzabin cizon sauro.

Yayin da yake kara haske akan fa’idar amfani da gidajen sauron don hana zazzabin cizon sauro, darektan cibiyar lafiya, Dr Omokhudu Idogho, yace wannan dabaran ya kasance mafi tattali kuma mafi sauki.

Idogho ya bayyana cewa kimanin dala miliyan 40 ne aka kashe wajen siyan gidajen sauro fiye da miliyan takwas da za a rarraba a Kano kadai.

KU KARATA KUMA: Buhari ya bani N30.8bn domin na biya basussukan albashi – Gwamna Bello

Ya roki kafofin yada labarai da su wayar da kan al’umma akan tasiri da kuma dabarun yin amfani da gidajen sauron don samun cikakkiyar amfani.

Wacce ta wakilci Babbar Ma’aikatar lafiya, Hajiya Fatima Bukar a wakilcinta tace tayi amfani da fasaha don tabbatar da gaskiya da kuma tasiri wajen tsarin rarrabawa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel