Yanzu-yanzu: Tawagar Buhari ta musamman ta dira kasar Afirka ta kudu

Yanzu-yanzu: Tawagar Buhari ta musamman ta dira kasar Afirka ta kudu

Tawagar da shugaba Muhammadu Buhari ya tura kasar Afirka ta kudu ta dira birnin Johannesburg, domin ganawa da shugaban kasar, Cyril Ramaphosa.

Wakilin shugaba Buhari na musamman shine shugaban hukumar leken asirin tarayya wato NIA, Ambasada Ahmed Abubakar.

Jakadan Najeriya zuwa Afrika ta kudu da sauran jami'an ofishin jakadancin sun tarbesa ne a babban filin jirgin saman O.R Tambo.

Ana sa ran zai gana da shugaban kasar Afirka ta kudu a birnin Pretoriya ranar Juma'a.

A ranar Talata, 3 ga Satumba, Ministan harkokin wajen Najeriya, Geofreey Onyeama ya bayyana cewa shugaba Buhari ya tura wakili na musamman kasar Afrika ta kudu domin ganewa idonsa ainihin abinda ke faruwa na kashe-kashen yan Najeriya a kasar.

Wannan rikicin ya haifar da kone-kone, sace-sace, da zanga-zanga a birane Legas da Abuja a kamfanonin mallakin gwamnatin kasar Afirka ta kudu.

Shoprite, kanti mafi girma a Najeriya ya fara fuskantar kalubale tun jiya kasancewar mallakan yan Afrika ta kudu ce.

A ranar Talata kadai, matasa sun kai hari kantin Shoprite a Legas da Ibadan.

A daren Talata, gwamnatin tarayya ta yi Allah wadai da matakin da yan Najeriya ke dauke na kai hari kasuwannin yan kasar Afrika ta kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel