Kano: Kotun zabe ta tabatar da nasarar Doguwa, Kofa da Nass

Kano: Kotun zabe ta tabatar da nasarar Doguwa, Kofa da Nass

Kotun sauraron kararrakn zaben majalisar dokokin tarayya da na jiha a jihar Kano, a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, ta jaddad nasarar Shugaban masu rinjaye majalisar wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben majalisar dokokin tarayya da aka yi a 2019.

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Air Commodore Salisu Shehu (rtd), ne ke kalubalantar Doguwa, wanda ya kasance mamba mai wakiltan mazabar Doguwa/Tudun Wada a majalisar tarayya, kan zargin yawan kuri’u da suka zarce ka’ida da kuma magudi zabe.

Da yake zartar da hukunci, kwamiti mutum uku na kotun zaben karkashin jagorancin Justis Nayai Aganaba, ya kori karar kan hujjar cewa masu karar sun gaza tabbatar da shari’arsa a gaban kotu, inda aka ci tararsu N300,000.

Da yake martani ga hukuncin, lauyan masu kara, Barista Ibrahim Isa Wangida, ya bayyana cewa za su yi nazari akan hukuncin sannan su ga ko akwai bukatar daukaka kara, za kuma su shawarci wadanda suke karewa.

A wani lamari makamancin haka, kotun da farko ta jaddada nasarar zaben Abdulmumini Jibril Kofa, mamba mai wakiltan mazabar Kiru/Bebeji.

Dan takarar PDP, Aliyu Datti Yako ne ke kalubalantar nasarar Kofa kan zargin cewa an samu yawan kuri’u da suka zarce ka’ida da kuma magudin zabe.

Kotun ta kori karar kan cewa wadanda ke karar sun gaza tabbatar da zarginsu yadda kamata ya gaban kotu.

Har ila yau, kotun zaben ta tabbatar da nasarar Hon. Sani Ma’aruf Nass, mamba mai wakiltan mazabar Minjibir/Ungogog.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya bani N30.8bn domin na biya basussukan albashi – Gwamna Bello

PDP da dan takararta, Muhammad Tajo Usman, sun shigar da kara kan zargin cewa Nass bai halarci makarantar sakandare ba, cewa an tsame dan takarar na PDP a lokacin zaben.

Kotun zaben da take yanke hukunci ta kori karar kan hujjar cewa masu karar su gaza tabbatar da zarginsu yadda ya kamata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel