Mai Mala Buni ya fara gina gidaje 3,600 don amfanin talaka a jahar Yobe

Mai Mala Buni ya fara gina gidaje 3,600 don amfanin talaka a jahar Yobe

Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni ya kaddamar da fara ginin sabbin gidaje guda 3,600, daga cikin ayyukan da ya kudurci aiwatarwa don murnar cikarsa kwanaki 100 a matsayinsa na gwamna, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jahar Yobe za ta samar da gidajen nan ne tare da hadin gwiwar kamfanin Family Homes Funds Limited, inda yace za’a gina gidajen ne a kananan hukumomi 17.

KU KARANTA: An samu rabuwar kai tsakanin wasu yan madigo yayin da ‘Mata’ ta harbe ‘Mijinta’

Gwamnan ya kara da cewa za’a samar da makarantu, asibitoci, wuraren ibadu, ofisoshin Yansanda, ofisoshin jami’an kashe gobara, kasuwanni da kuma filayen wasannin yara a cikin wadannan rukunin gidaje.

“Manufarmu ita ce jama’an jahar Yobe sun samu matsuguni masu armashi, kuma wanda zasu iya mallaka, haka zalika zamu tabbata an yi amfani da kayan aikin da ake samarwa a jahar Yobe don gina wadannan gidaje.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan ya yi kira ga hukumar kula da gidaje da kadarori ta jahar tare da ma’aikatar filaye da gidaje ta jahar Yobe dasu sanya idanu a kan yan kwangilar don tabbatar da sun yi aikin daya kamata.

A wani labarin kuma, majalisar dokokin jahar Osun ta baiwa hukumomin tsaron jahar umarnin kama duk wani mahaluki da suka kama yana busa taba sigari a tsakiyan jama’a domin hukuntashi kamar yadda sabuwar dokar haramta shan sigari ta tanadar.

Kaakakin majalisar, Timothy Owoeye ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Alhamis a garin Osogbo, babban birnin jahar Osun, wannan umarni ne a daidai lokacin da kungiyoyi masu zaman kansu suke gudanar da hidindimun tunawa da ranar yaki da cututtuka da ake iya dauka daga mutum zuwa mutum na shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel