Dan gidan tsohon shugaban kasar Misra Abdullahi Morsi ya mutu a asibiti dalilin bugun zuciya

Dan gidan tsohon shugaban kasar Misra Abdullahi Morsi ya mutu a asibiti dalilin bugun zuciya

- Dan gidan marigayi tsohon shugaban kasar Misra Mohamed Morsi ya mutu shima a asibiti

- Abdullahi Morsi ya mutu ne jiya Laraba a birnin Cairo sanadiyyar bugun zuciya da ya gamu da ita

- Haka shima mahaifinsa Mohamed Morsi ya mutu a ranar 17 ga watan Yunin wannan shekarar a lokacin da yake tsare a gidan yari

Dan Autan marigayi tsohon shugaban kasar Misra (Egypt) Mohamed Morsi ya mutu sanadiyyar bugawar zuciya da ya samu a wani asibiti dake Cairo, jaridar Al Jazeera ta ruwaito.

Abdullahi Morsi wanda yake matashi ya mutu jiya Laraba a asibitin Oasis dake Giza a yankin kudu maso yammacin birnin kasar.

Daya daga cikin 'yan uwan marigayin shine ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu, amma bai bayar da ainahin abinda ya faru ba. Haka kuma ma'aikatar lafiya ta kasar ba ta ce komai kan lamarin ba.

KU KARANTA: Tashin hankali: Wata mata ta kashe mijinta ta hanyar yanke masa kai da mazakuta ta bai wa karnukanta suka cinye

Mohamed Morsi, shugaban farar hula na farko a kasar Misra ya mutu ranar 17 ga watan Yunin wannan shekarar, a lokacin da ake tsare dashi akan wani laifi da ake ganin siyasace karara tasa aka kama shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel