Buhari ya bani N30.8bn domin na biya basussukan albashi – Gwamna Bello

Buhari ya bani N30.8bn domin na biya basussukan albashi – Gwamna Bello

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba shi tallafi na kimanin naira biliyan 30.8 don biyan bashin albashin ma’aikata dake jihar.

Yahaya Bello dage cewa a halin yanzu ba a bin gwamnatinsa bashi albashi domin tana biyan ma’aikata duk wata.

Gwamnan wanda yayi jawabi ga manema labarai bayan ganawar da yayi da kwamitin Jam’iyyar APC na kasa da kuma wadanda suka nemi takaran zaben fidda gwani na gwamna, har ila yau ya bukaci jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ta dubi cikin gida don gano wadanda suka kai hari harabar inda ta gudanar da zaben fidda gwaninta ba tare da daura mishi laifi ba.

Ya bayyana cewa: “Dangane da labaran da ake yadawa cewa ma’aikata na bin jihar Kogi albashi, ina son in jaddada muku cewa, na gaji bashin albashin daga shuwagabanni biyu da suka gabata.

“Matsala ce da na gada a lokacin da na hau mulki, amman ina son in sanar da ku a yau cewa ma’aikata basu bin Kogi bashin albashi."

Yayin da yake mayar da martani akan zargin da PDP tayi cewa yana da hannu cikin harin da aka kai mata yayin gudanar da zaben fidda gwanin ta, Bello yace “mamban jam’iyyar APC ne ni ba na PDP ba.”

KU KARANTA KUMA: APC ta bawa Buhari shawara a kan matakin da ya kamata ya dauka a kan MTN, Shoprite da DSTV

Akan sakamakon ganawarsu da kuma tabbaci da ya samu, yace: “Duk yan’uwana maza da mata sun amince zasu mara mun baya, kuma zasu taimaka mun a zaben dake gabatowa don tabbatar da cewa APC tayi nasara a jihar Kogi da kuma cigaba da samar da sakamakon damokardiyya ga mutanenmu."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel