APC ta bawa Buhari shawara a kan matakin da ya kamata ya dauka a kan MTN, Shoprite da DSTV

APC ta bawa Buhari shawara a kan matakin da ya kamata ya dauka a kan MTN, Shoprite da DSTV

Jam'iyyar APC ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun mallaki kamfanoni da masana'antu mallakar kasar Afrika ta Kudu.

Manyan kamfanonin kasar Afrika ta Kudu dake aiki a Najeriya sun hada da kamfanin sadarwa na MTN, kamfanin tashohin tauraro na DSTV, babban shagon cinikayya na 'Shoprite' da sauransu.

Kazalika, jam'iyyar ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kwace lasisin dukkan wasu bankuna mallakar 'yan kasuwar kasar Afrika ta Kudu dake aiki a Najeriya.

Irin wadannan bankuna sun hada da 'Stanbic IBTC da 'Standard Chartered'

Jam'iyyar ta bayar da wannan shawara ne yayin wani taron gaggawa na kwamitin gudanarwarta da ta yi ranar Alhamis a Abuja.

Yanzu haka kamfanin MTN da na DSTV sun bayar da umarnin rufe ofisoshinsu dake manyan biranen Najeriya biyo bayan fara kai musu hare-haren daukan fansa sakamakon harin da 'yan kasar Afrika ta Kudu ke cigaba da kai wa 'yan Najeriya da wuraren kasuwancinsu a kasar su.

DUBA WANNAN: Dan takarar gwamna a PDP ya canja sheka zuwa APC

Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewa an rufe ofishin MTN na Kano dake Nasarawa GRA bisa umarnin da aka aiko wa ofishin daga sama, saboda akwai isassun jami'an tsaro dake gadin ofishin tun bayan fara kai hare-haren daukar fansa a ranar Talata.

Jaridar Solacebase.com ta ce wakilinta ya ga jami'an tsaro sun kwace wayar wani matashi da ya yi kokarin daukan hoton ofishin a ranar Laraba.

Kazalika, jaridar ta ce wakilinta da ya ziyarci ofishin kamfanin DSTV, ya ga motoci biyu na jami'an 'yan sanda da wata mota guda ta jami'an hukumar NSCDC da aka fi kira da 'civil defence'.

Jaridar ta ce hatta a cikin sakon da kamfanin MTN ya aike mata, ya sanar da cewa sun rufe shagunan a yau (Laraba) tare da bayyana cewa za a iya samun su a kan manhajar Tuwita a kan sunan 'MTN180'

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel