Rundunar yan sanda ta ceto mutane 22 da aka yi garkuwa da su, ta gurfanar da masu laifi 72 a Imo

Rundunar yan sanda ta ceto mutane 22 da aka yi garkuwa da su, ta gurfanar da masu laifi 72 a Imo

Tawagar yan sanda na Operation Puff Adder a jihar Imo a ranar Alhamis, 5 ga wata Satumba, sun gurfanar da mutane 72 da ke da hannu a laifuka daban-daban da aka aikata kwanan nan a jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar, Rabiu Ladodo ya bayyana cewa an kama masu laifin ne a yankuna daban-daban a jihar cikin makonni shida da suka gabata.

Har ila yau an kama wani mamban na kungiyar miyagu masu yiwa mata fyade, Stanley Ebere wanda ya kasance da hannu cikin fyade da aka yi ma wata yarinya yar shekara 11 a gaban sauran mambobin kungiyar.

A cewar shi, farautan yan fashi a jihar ya kasance manufar “Operation Puff Adder” wanda Sufeto Janar na yan sanda ya kaddamar, wanda yace har ila yau tana nan daram.

Ya kara da cewa an ceto wasu mutane 22 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kwato motoci 11 a cikin haka.

Ladodo ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka gurfanar akwai mambobin kungiyar gawurtaccen mai garkuwa da mutanen nan da ya shahara a harkar sace kananan yara daga gidajen su, wasu lokuta cikin dare.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman kwamitin tsaro

An kama masu laifin, Chukwuemeka Onyebuchi (43) da Aina Nwachukwu mai shekaru 45 ne bayan an samu labarin sun sace kananan yara biyu, Oluwa Chukwu Opanwa (4) da Promise Opanwa (2), duk daga iyaye guda a Umuobum a yankin Kudancin Karamar hukumar Ideato dake jihar.

A cewar kwamishinan yan sanda, rundunar yan sandan na nan tana bin duddugen mambobin kungiyar da suka tsere; yayin da ake kokarin ganin an kubutar da yaran da aka sace.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel