Makarantu 1,320 ne za su amfana da tallafin kudi na bankin duniya daga jihar Bauchi

Makarantu 1,320 ne za su amfana da tallafin kudi na bankin duniya daga jihar Bauchi

- Makarantu 1,320 ne zasu amfana da shirin tallafin kudi na bankin duniya daga jihar Bauchi

- Shirin an yi shi ne don kawo gyara ga makarantun gwamnati

- Gwamnan jihar yace gwamnatin shi shirye take da ba wa 'yan jihar ilimi ingantacce

Muhammad Umar, shugaban shirin bankin duniya na cigaban makarantu na shekarar 2019, reshen jihar Bauchi, ya ce makarantu 1,320 daga kananan hukumomi 5 na jihar ne zasu amfana da shirin.

A ranar Laraba da ya yi magana da manema labarai a jihar Bauchi, Umar ya ce an shirya tallafin ne don daukar nauyin gyaran makarantu, gyaran kujeru na makarantu don inganta harkar ilimi.

Umar ya lissafo kananan hukumomin da zasu amafana da shirin. Sun hada da Zaki, Shira, Ganjuwa, Katagum da Toro.

Shugaban shirin na jihar yace an dau matakan daukar nauyin aiyukan tare da tsarin da za su tabbatar da cewa an aiwatar da aiyukan.

DUBA WANNAN: Bera ya jefa ango a mummunan hali

Ya kara da cewa, shirin anyi shi ne don karfafa makarantun gwamnati.

Da yayi jawabi bayan mika cheque din kudi har N500,000 ga duk makarantun da suka amfana, Gwamna Bala Mohammed ya yi alkawarin cigaba da inganta ilimi a matsayin hanyar kawo karshen barin makaranta da yara keyi.

Ya ce gwamnatinsa ta maida hankali ne wajen dawo da martabar ilimi a jihar, ta hanyar samar da ababen more rayuwa, gyaran makarantu da horar da malamai.

"Gwamnatin yanzu ta maida hankali ne wajen gyara bangaren ilimi don cimma manufarmu ta ganin cigaban yara 'yan makarantun gwamnati."

"Muna tabbatar muku da cewa a shirye muke don samar da ilimi mai inganci ga duk 'yan jihar."

"Ina horar duk makarantun da suka amfana, da su yi amfani da tallafin kudin nan wajen gyare-gyare a makarantu don tabbatar da samuwar ilimi mai inganci," cewar gwamnan

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel