Rushe Masallaci: Gwamna Wike ya gayyaci kwamitin 'Ulama' da gwamna Matawalle

Rushe Masallaci: Gwamna Wike ya gayyaci kwamitin 'Ulama' da gwamna Matawalle

- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya gayyaci takwaransa na jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, zuwa Fatakwal

- Wike ya gayyaci Matawalle ne a kan 'sa toka sa katsin' da ake yi a kan zargin gwamnatin jihar Ribas da rushe wani Masallaci

- Gwamna Matawalle ya ce zai amsa gayyatar da Wike ya yi masa, zai ziyarci jihar tare da mambobin kwamitin 'Ulama'

A yayin da har yanzu ake cigaba da musayar yawu a kan batun zargin gwamnatin jihar Ribas da rushe wani Masallaci birnin Fatakwal, gwamnan jihar, Nyesom Wike, ya gayyaci takwaransa na jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, zuwa jihar Ribas.

Gwamna Matawalle ne ya sanar da hakan ranar Litinin, 2 ga watan Satumba, yayin da ya karbi bakuncin wasu malaman addinin Isalama a fadarsa domin taya shi murnar cika kwanaki 100 a kan karagar mulki.

DUBA WANNAN: An yanke wa wasu dakarun NAF biyu hukuncin dauri da aiki mai tsanani a gidan yari

Matawalle ya bukaci Malaman su kwantar da hankalinsu tare da shaida musu cewa ya yi magana da gwamna Wike ta wayar tarho, sannan ya kara da cewa zai tafi da wasu daga cikin Malaman zuwa Ribas yayin da zai ziyarci jihar domin amsa gayyatar da gwamna Wike ya yi masa, inda zasu tattauna domin warware matsalar cikin sauki.

Gwamna Wike da Matawalle 'yan jam'iyyar PDP ne.

Malaman da suka ziyarci gwamnan sun bayyana muhimmancin zaman lafiya tare da yin amfani da sulhu wajen warware kowacce irin matsala. Kazalika, sun yi kira ga jama'a da su zauna lafiya da juna ba tare da kokarin nuna banbancin kabila, bangare ko addini ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel