Yan bindiga sun kashe wata mata sun yi garkuwa da matafiya 12 a hanyar Abuja

Yan bindiga sun kashe wata mata sun yi garkuwa da matafiya 12 a hanyar Abuja

Wasu gungun yan bindiga marasa Imani sun yi garkuwa da dimbin fasinjoji har guda 12 dake tafiya a kan hanyar Abuja zuwa garin Lokojan jahar Kogi, bayan sun kashe wata mata guda daya, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun tare fasinjojin ne a cikin wata babbar motar bas mai cin mutane 18 a daidai kauyen Omoko, kimanin kilomita 4 zuwa garin Abaji dake kan iyakar Abuja da jahar Kogi.

KU KARANTA: An kashe mutum 1 a sanadiyyar rikici tsakanin manoma da makiyaya a Jigawa

Wani shaidan gani da ido ya shaida ma majiyarmu cewa yan bindigan sun dakatar da motar fasinjojin ne, inda nan tare suka dirka ma wata mata bindiga har lahira, sa’annan suka yi awon gaba da sauran fasinjoji 12 cikin daji.

Shima wani matafiyi daya tsallake rijiya da baya, amma yan bindigan sun harbeshi a ciki, mai suna Adesoji Rufus ya ayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Satumba da misalin karfe 4 na rana a lokacin da ya yi haramar zuwa Legas daga Abuja.

Rufus ya bayyana cewa yana cikin kotarsa kirar Toyota Sienna ne lokacin da yan bindigan suka hauro kan titi, nan da nan suka shiga bude ma motoci wuta irin harbin mai kan uwa da wabi, daga nan motars ta kufce, sa’annan suka kwashe mutane biyu daga cikin motarsa.

“Yan bindigan sun tare hanyar tsawon mintuna 30 ba tare da wasu jami’an tsaro sun bayyana a wajen ba, sai daga bisani wasu jami’an hukumar Civil Defence suka isa wajen inda suka ceci wadanda yan bindigan suka sassara, tare da mikasu zuwa asibiti.." Inji shi.

Sai dai kaakakin hukumar Yansandan jahar Kogi, Williams Aya ya bayyana lamarin a matsayin harin yan fashi da makami, inda yace yayin da yan fashin suka hangi Yansanda sai suka tsere, sa’annan ya musanta rahoton yin garkuwa da mutane 12.

Game da matar da ta mutu kuwa, ya bayyana cewa ta diro ne daga motar da take ciki, a sanadiyyar haka wata mota dake tahowa ta hannun da ta diro ta bi ta kanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel