Mummunan hatsarin mota ya cika da daliban makarantar sojoji 12 a Kaduna

Mummunan hatsarin mota ya cika da daliban makarantar sojoji 12 a Kaduna

Wasu daliban makarantar sojoji 12 sun ji rauni daban-daban bayan motar da suke tafiya a ciki yayi karo da dogon iccen fal-waya a hanyar Independence Way dake Kaduna.

Daliban na tafiya ne a wani motan bas mai zaman mutane 18 mallakar kungiyar daliban makarantar Polin jihar Kaduna lokacin da hatsarin ya afku da misalin karfe 1:30 na ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Anyi gaggawan kwasan wadanda suka jikkata zuwa asibitin sojoji.

Maza da matan da suka jikkata duk sanye suke a kayan sojoji.

Daya daga cikin daliban da suka jikkata yace: “Mun fito ne daga makarantar sojojin Najeriya, Zaria. Mun zo makarantar Poli da ke Kaduna daga cikin horonmu na NMS na 2019 na mako guda.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta sake umurtan Atoni Janar na tarayya da EFCC da su janye daga daukar mataki akan kadarorin Yari

"A hanyarmu na dawowa Zaria sai tayar motan ya fashe sannan motan ya bigi fal-waya. Ba a rasa rai ba amma mutane daga cikinmu sun ki mummunan rauni,” inji shi.

A wani lamarin kuma mun ji cewa, ttubabbun 'yan bindiga a Katsina sun sanar da gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, cewa wasu daga cikin jami'an rundunar 'yan sanda da dakarun sojin Najeriya ne ke rura wutar aiyukan ta'addanci a jihar domin kawai su samu kudi.

Sun yi gargadin cewa matukar jami'an tsaron basu daina karbar kudi da shanu a hannunsu ba, ba za a samu wani canji ta fuskar samun zaman lafiya ba a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel