Yan majalisu sun bada umarnin kama duk mai shan sigari a bainar jama’a

Yan majalisu sun bada umarnin kama duk mai shan sigari a bainar jama’a

Majalisar dokokin jahar Osun ta baiwa hukumomin tsaron jahar umarnin kama duk wani mahaluki da suka kama yana busa taba sigari a tsakiyan jama’a domin hukuntashi kamar yadda sabuwar dokar haramta shan sigari ta tanadar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kaakakin majalisar, Timothy Owoeye ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Alhamis a garin Osogbo, babban birnin jahar Osun.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 2 a wasu hare hare da suka kai a Borno

Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar ta bayar da wannan umarni ne a daidai lokacin da kungiyoyi masu zaman kansu suke gudanar da hidindimun tunawa da ranar yaki da cututtuka da ake iya dauka daga mutum zuwa mutum na shekarar 2019.

Wani babban likita mai suna Adeniyi Oginni ya bayyana ma yan majalisun cewa akalla mutane miliyan 39.5 ne suke mutuwa a duk shekara a dukniya a sanadiyyar ire iren wannan cututtuka, kimanin kashi 65 kenan na mace mace.

Likitan ya kara da cewa cututtuka kamar su hanawan jini, cutar lakka, cutar daji, ciwon siga, cututtukan da suka danganci hanyar wucewar iska a jikin mutum, cutar sikila, ciwuwwukan hauka na daga cikin irin cututtukan da kungiyarsu take kokarin yaki dasu a tsakanin al’umma.

A wani labari kuma, wani dan majalisar wakilai daga jahar Cross Rivers, kuma kusa a jam’iyyar APC, Alex Egbona ya rasa kujerarsa sakamakon wani hukunci da kotun sauraron korafe korafe ta yanke a ranar Laraba, 4 ga watan Satumba a garin Calabar.

Tsohon kaakakin majalisar dokokin jahar Cross Rivers, kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019, John Gaul-Leo ne ya shigar da karar Alex inda ya kalubalanci nasarar daya samu a zaben ranar 23 ga watan Feburairu na 2019.

Kotun bayyana Alex a matsayin haramtaccen wakilin mazabar Abi/Yakurr a na jahar Cross Rivers a majalisar wakilan Najeriya, inda ta bayyana cewa tun farko ba Alex bane halastaccen dan takarar jam’aiyyar APC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel