Kotu ta sake umurtan Atoni Janar na tarayya da EFCC da su janye daga daukar mataki akan kadarorin Yari

Kotu ta sake umurtan Atoni Janar na tarayya da EFCC da su janye daga daukar mataki akan kadarorin Yari

Babban kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, ta jadadda hukuncinta da ke umurtan Atoni Janar na tarayya da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), da kada su ci gaba da yunkurinsu na kwace kadarorin tsohon gwamnan jihar Zamfa, Abdulaziz Yari.

Justis Nkeonye Maha ya jadadda cewa yin haka ba zai zamo adalci ba a yanzu da lamarin ke jingine a gaban kotu.

A halin yanzu, kotun ta yi umurnin cewa a tura takardar shari’an zuwa mukaddashin Shugaban alkalin babban kotun tarayya, Justis John Tsoho, domin a sake gabatar dashi ga kotu, duba ga lokacin hutun kotu da zai kare a ranar 13 ga watan Satumba.

Don haka, a yanzu a dage shari’an zuwa ranar 30 ga watan Satumba doin sauraron karar.

A lokacin shari’an a ranar Alhamis, lauyan tsohon gwamnan, Mahmud Magaji (SAN), ya sanar da kotu cewar EFCC ta gabatar masa da takardar rantsuwa a kotu, wanda ya rigada ya mayar da martani.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fursunoni 2,742 ke a jerin wadanda aka yanke wa hukuncin kisa

Sai dai, lauyar hukumar, Hussaina Gambo, a nemi a dage shari’an domin bata dammar hada wasu takardun kotu.

A nashi bangaren Atoni Janar na tarayya, wanda aka ambata a matsayin mutum na farko da ake kara, bai halarci kotun ba sannan kuma bai samu wakilcin lauyansa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel