Da duminsa: Dan takarar gwamna a PDP ya canja sheka zuwa APC

Da duminsa: Dan takarar gwamna a PDP ya canja sheka zuwa APC

Dan takarar gwamnan jihar Bayelsa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben da za a yi a watan Nuwamba, Mista Great Joshua Maclver, ya canja sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin gwamnatin tarayya.

Canjin shekar dan takarar na zuwa ne a cikin kasa da sa'o'i 24 bayan Mista Maclver ya sha kasa a zaben fidda dan takara a hannun Sanata Douye Diri, wanda ya samu nasarar zama dan takarar gwamnan jihar Bayelsa a jam'iyyar PDP.

A cewar Maclver, ya koma jam'iyyar APC ne don ya hada gwuiwa da dan takarar jam'iyyar APC, Cif David Lyon, a zaben da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba domin kawar da jam'iyyar PDP daga jihar Bayelsa.

DUBA WANNAN: Babban dan sanda daya ya mutu, uku sun samu rauni bayan kama yaran Wadume

A wata takarda da ya aike wa shugaban jam'iyyar APC a mazabarsa, Olodiama 4, dake Yenogoa, babban birnin jihar Bayelsa, dan takarar ya ce ya koma jam'iyyar APC ne saboda wasu dalilai na kashin kansa.

Mista Maclver ya yi godiya ga jam'iyyar PDP bisa bashi damar zama daya daga cikin 'yan siyasar da suka assasa jam'iyyar a jihar Bayelsa tun daga matakin mazaba har zuwa sama.

Tuni shugaban mazabar Mista Maclver na jam'iyyar APC ya karbe shi hannu bibiyu tare da bashi katin jam'iyya bayan ya cika dukkan ka'idojin zama mamba a jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel