Gwamnatin jihar Zamfara za ta kashe Naira biliyan 8.631 don gina RUGA a jihar

Gwamnatin jihar Zamfara za ta kashe Naira biliyan 8.631 don gina RUGA a jihar

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce gwamnatin jiharsa za ta kashe Naira biliyan 8.631 don gina RUGA

- Ya sanar da hakan ne yayin fara zuba fandishon ginin daya daga cikin RUGA uku a karamar hukumar Maradun

- Za a wadata RUGA da makarantun boko, islamiya, kasuwa, wajen kiwo, masallatai da sauran ababen more rayuwa

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce za ta kashe Naira biliyan 8.631 don gina Ruga a jihar.

Gwamna Bello Matawalle ya sanar da hakan ne ranar Laraba yayin da aka fara gina daya daga cikin RUGA uku da za a yi a jihar.

Ya ce za a gina RUGA uku ne a jihar, kowacce kuma a mazaba daya. Ginin kowacce daya zai ci naira biliyan 2.877.

Kamar yadda ya sanar, kowacce RUGA zata samu gidaje 210 masu dakunan barci bibbiyu da uku-uku, makarantar boko da islamiyya, wajen kiwo da masallatai.

DUBA WANNAN: Bera ya jefa ango a mummunan hali

Sauran abubuwan da za a samar sun hada da ofishin 'yan sanda, shaguna 130, karamar kasuwa, kasuwar dabbobi, wajen tatsar nonon dabbobi, tituna da magudanen ruwa.

Matawalle, ya yi murnar kwanaki dari a kujerar gwamnan jihar ta hanyar shimfida fandishon RUGA. Ya ce za a samar da cibiyoyin lafiya ga Fulanin da kuma dabbobinsu a duk fadin jihar.

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, ya ce an kirkiro da RUGA tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka don cigaban kiwon dabbobi da noma.

Ya kwatanta rikicin Fulani makiyaya da manoma da abu mara dadi. Gina RUGA da gwamnatin Zamfara za ta yi zai taka rawar gani wajen kawo karshen fadan da ke aukuwa a jihar.

"A jihar Sokoto, ina da RUGA 19, 10 daga cikin suna da ababen more rayuwa na zamani, wadanda zamu cigaba ingantawa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel