Kotu ta tsare wani matashi akan kona kujerar da mahaifinsa yafi so

Kotu ta tsare wani matashi akan kona kujerar da mahaifinsa yafi so

Wata kotun Kubwa da ke Abuja a ranar Alamis, 5 ga watan Satumba, tayi umurnin tsare wai matashi dan shekara 27 mai suna, Mareous Irabor, wanda ya amsa laifinsa nakona kujerar da mahaifinsa yafi so, a gidan gyara hallaya, zuwa lokacin da za a zartar masa da hukunci.

Alkalin, Ibrahim Balarabe ya bayar da umurni, bayan an kama Irabor da laifin tayar da hankalin jama’a da kuma haddasa barna da wuta.

Balarabe ya dage sauraron shari’an zuwa ranar 16 ga watan Satumba.

Dan sanda mai kara, John Okpa ya fada ma kotu cewa Irabor Paul yya kai rahoton lamarin ofishin yan sanda da ke Kubwa a ranar 26 ga watan Agusta.

Yace dan mai karan ya cinna wa kujerar mahaifinsa da yafi so wuta, sannan a lalata talbijin da wasu muhimman abubuwa da kudinsu ya kai N39,300.

Laifin ya saba ma sashi na 114 da 337 na doka.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman kwamitin tsaro

A wani lamarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Kwaturola Janar na hukumar gyara hallayar mutane na Najeriya wacce aka fi sani da hukumar gidan yari, Jafa’aru Ahmed ya bayyana cewa a yanzu haka fursunoni 2,742 ne cikin jerin wadanda aka yanke wa hukuncin kisa a Najeriya.

Ya tabbatar da cewar hukumomin da suka kamata na aiki akan hukunci kan ko a amince da zartar da hukuncin kisan a kansu ko kuma a mayar dashi zuwa hukuncin daurin rai-da-rai.

Ya yi Magana ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, a wani taron manema labarai kan dokar hukumar wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar a watan Yuli.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel