Yanzu Yanzu: Fursunoni 2,742 ke a jerin wadanda aka yanke wa hukuncin kisa

Yanzu Yanzu: Fursunoni 2,742 ke a jerin wadanda aka yanke wa hukuncin kisa

Kwaturola Janar na hukumar gyara hallayar mutane na Najeriya wacce aka fi sani da hukumar gidan yari, Jafa’aru Ahmed ya bayyana cewa a yanzu haka fursunoni 2,742 ne cikin jerin wadanda aka yanke wa hukuncin kisa a Najeriya.

Ya tabbatar da cewar hukumomin da suka kamata na aiki akan hukunci kan ko a amince da zartar da hukuncin kisan a kansu ko kuma a mayar dashi zuwa hukuncin daurin rai-da-rai.

Ya yi Magana ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, a wani taron manema labarai kan dokar hukumar wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar a watan Yuli

KU KARANTA KUMA: Watan Agusta: Rayuka 53 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 73 a fadin Najeriya

Idan dai ba za kumanta ba a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan dokar sauya tsarin gidan yari.

Hakan ya haifar da canja wa hukumar ta gidajen yari suna, zuwa hukumar gidajen gyara halayen ‘yan Najeriya.

Tun cikin watan Janairu, 2008 ne Sanata Victor Ndoma-Egba ya gabatar da kudirin lokacin ya na sanata, sai dai kuma hakan bai yiwu a sai a 2019 dinnan aka sanya masa hannu ya zama doka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel