Wata sabuwa: Yan sanda ne suka yi garkuwa dani, suka nemi na basu duka kudin banki na ko su kashe ni - Mawaki Ikechukwu

Wata sabuwa: Yan sanda ne suka yi garkuwa dani, suka nemi na basu duka kudin banki na ko su kashe ni - Mawaki Ikechukwu

- Wani sabon mawaki mai tashe a jihar Legas ya bayyana cewa 'yan sanda ne suka kama shi a jihar ta Legas

- Ya bayyana cewa sun nemi ya basu duka kudin da ke cikin asusun shi, ko kuma su kashe shi a wajen babu wanda zai sani kuma

- Ya bayyana cewa a jikin kakinsu babu suna ko lamba, amma kuma tabbas kayan 'yan sanda ne

Wani sabon mawaki da yake tashe a wannan lokacin, Ikechukwu ya bayyana wani abu da jami'an hukumar 'yan sanda na jihar Legas suka yi mishi wanda bai ji dadin shi ba.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, mawakin ya ce: "Jami'an 'yan sanda ne suka yi garkuwa dani a daren jiya, tafiyar mintuna biyu kawai zuwa gidana, suka kai ni wani wuri suka nemi na cire musu komai na cikin asusuna ko kuma su kashe ni babu kuma wanda zai sani."

"Ba 'yan fashi bane, kowanne a cikinsu rike yake da bindiga mai kirar AK 47, sun daure ni a jikin motarsu."

KU KARANTA: Tirkashi: NANS ta bai wa 'yan kasar Afrika ta Kudu kwana hudu su tattare kayansu su bar Najeriya

"Kuma da anyi magana sai kuce gwamnati tana yin aiki, bari na fada muku wani, duk wanda yake yin dare a garin nan, idan har 'yan sanda suka kama ka, to shikenan ka gama. Babu suna ko lamba a jikin kakinsu.

"Bayan sun gama karbe duka kudina sai suka fara dariya suna cewa wai bana jin magana, wai yaushe zan kai su wajen Don Jazzy. Hakan ya nuna mini cewar sun sanni.

"Bayan sun gama cin zarafi na na hau motar haya na koma gida."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel