Tirkashi: NANS ta bai wa 'yan kasar Afrika ta Kudu kwana hudu su tattare kayansu su bar Najeriya

Tirkashi: NANS ta bai wa 'yan kasar Afrika ta Kudu kwana hudu su tattare kayansu su bar Najeriya

- Kungiyar dalibai ta kasa ta bai wa 'yan kasar Afrika ta Kudu da suke zaune a Najeriya kwanaki hudu su bar Najeriya

- Kungiyar ta ce ba za ta iya jiran shugaban kasa Muhammadu Buhari ba wanda har yanzu ya kasa daukar wani kwakkwaran mataki

- Kungiyar ta sanya dokoki guda uku wanda ta bayyana dole 'yan kasar Afrika ta Kudu su bi kafin a zauna lafiya

Kungiyar dalibai ta Najeriya (NANS) ta bai wa 'yan kasar Afrika ta Kudu da suke zaune a Najeriya daga yau zuwa ranar Litinin 9 ga watan Satumaba, 2019 da su tattare komatsansu su fice daga Najeriya.

Kungiyar ta bayyana wannan sanarwar ne bayan harin da 'yan kasar Afrika ta Kudu suka dinga kaiwa 'yan Najeriya da suke zaune a kasar ta Afrika ta Kudu.

A cewar jami'in hulda da jama'a na kungiyar daliban, Azeez Adeyemi, wanda yayi magana a maimakon kungiyar, ya ce kunginyar ba za ta jira har sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki mataki ba akan lamarin.

Ga abinda ya ce: "Bacin ran 'yan Najeriya, ya kai makura akan irin abinda 'yan kasar Afrika ta Kudu suke yiwa 'yan Najeriya da suke zaune a can.

KU KARANTA: An yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama shi da laifin kashe budurwarsa

"A matsayinmu na dalibai, munyi kokari mu manta da duk abubuwan da suka faru a baya tsakaninmu da 'yan Afrika ta Kudu, amma kamar hakan ba zai yiwu ba domin kuwa wadannan dabbobin sun nuna mana baza su daina abinda suke yi ba har sai mun dauki mataki akai.

"A matsayin mu na matasa, wanda nan gaba kasar hannunmu za ta dawo, ba zamu jira shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda har yanzu yaki ya dauki wani kwakkwaran mataki akan wannan lamari ba.

"Da farko kowane dan kasuwa da yake dan kasar Afrika ta Kudu dole ya daina kasuwancin sa daga nan zuwa awa 12.

"Na biyu duka manyan kamfanoni da kasar Afrika ta Kudu da suke aiki a Najeriya dole su rufe. Na karshe kuma duka 'yan kasar Afrika ta Kudu da suke zaune a Najeriya mun basu daga nan zuwa ranar Litinin su tattare kayansu su bar Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel