Shugaba Buhari ya jagoranci zaman kwamitin tsaro

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman kwamitin tsaro

A yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman kwwamitin tsaro a fadar Shugaban kasa a yau Alhamis, 5 ga watan Satumba.

Kwamtin ya hada da shugabannin hukumomin tsaro a kasar, kamar su Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; Shugaban hafsan sojoji, Laftanal Janar Tukur Buratai; Shugaban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe-Ibas; da kuma Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Abubakar Sadique.

Sauran sun hada da Sufeto janar na yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu; Darakta Janar na hukumar tsaro na sirro (DSS), Yusuf Bichi; da Darekta Janar na hukumar leken asiri (NIA), Ahmed Rufai.

KU KARANTA KUMA: Ganin hotunan El-Rufai, Fayemi da Sarkin Kano a Afrika ta Kudu ya fusata Jama’a

A wani labarin kuma mun ji cewa, rayukan al'umma musamman a Arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar barazana a sanadiyar munanan hare-hare na ta'addancin masu garkuwa da mutane, rikicin makiyaya da manoma, hare-haren 'yan daban daji da kuma kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

A wani rahoto da jaridar Premium Times ta ruwaito, akalla rayukan mutane 53 sun salwanta a sanadiyar aukuwar munanan hare-hare, yayin da mutane 73 suka afka tarkon masu garkuwa a fadin Najeriya cikin watan Agustan da ya gabata.

Sai dai cikin wannan sabuwar kididdiga da aka fitar, an samu rangwami na adadin rayukan da suk salwanta a sanadiyar aukuwar hare-hare cikin watan Agusta idan an kwatanta da watannin da suka shude a baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel