Ganin hotunan El-Rufai, Fayemi da Sarkin Kano a Afrika ta Kudu ya fusata Jama’a

Ganin hotunan El-Rufai, Fayemi da Sarkin Kano a Afrika ta Kudu ya fusata Jama’a

Jama’an da ke ziyarar shafukan sada zumunta za su ga yadda mutanen Najeriya ke ta faman banbami bayan da su ka gano cewa wasu daga cikin gwamnoninsu, su na kasar Afrika ta Kudu.

A daidai wannan lokaci da ake kokarin kashe wutar rikicin da ta tashi a kasar ta Afrika ta Kudu, wanda har gwamnatin Najeriya ta fasa zuwa taron WEF, sai aka ji cewa wasu gwamnoni su na kasar wajen.

Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da Takwaransa na Ekiti, Dr. Kayode Fayemi su na kasar wajen. Wani Hadimin El-Rufai ya karyata cewa wannan taro na WEF ya kawo su kasar.

Haka zalika ana rade-radin Mai martaba Sarkin Birnin Kano kuma tsohon gwamnan babban banki, Muhammadu Sanusi II ya na kasar Afrika ta Kudu domin halartar wannan babban taro na tattalin arziki.

KU KARANTA: Afrika ta Kudu ta rufe ofishin Jakadancinta da ke Najeriya

Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna wasu hotunsa inda ya ke ganawa da wasu kwararru a Birnin Pretoria domin jawowa jiharsa masu zuba hannun jari da buda kamfanoni da za su taimakawa jihar.

Hakan na zuwa ne bayan wani Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya soki Madam Oby Ezekwesili na halartar wannan taro na WEF bayan mataimakin shugaban kasa ya fasa wakiltar Najeriya.

Abin da ya faru kwanan nan na kashe ne ya jawo kasashe su ka yi baya-baya da kasar ta Afrika ta Kudu. Wannan ya sa aka rika sukar Ezekwesili, sai kuma aka ga ashe gwamnonin APC su na kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel