Dadiyata: ‘Dan takarar PDP a Kano, ya nemi ‘Yan Sanda su zage dantse

Dadiyata: ‘Dan takarar PDP a Kano, ya nemi ‘Yan Sanda su zage dantse

Idan ku na biye da mu, ku na da labari cewa fiye da wata guda kenan da aka sace wani fitaccen Matashi ‘Dan adawar gwamnati a cikin Garin Kaduna. Har yanzu babu labarin halin da yake ciki.

‘Dan takarar jam’iyyar PDP na zaben gwamna a jihar Kano, Abba Kabiru Yusuf, ya ce tun da aka sace Matashin nan, Abubakar Idris watau Dadiyata, su ke bakin kokarin gano inda aka kai shi.

Injiniya Abba Yusuf ya koka da yadda bacewar wannan Bawan Allah mai sukar gwamnatin APC wanda ya kira na su yake daukar dogon lokaci ba tare da jami’ai sun iya gano inda yake ba.

‘Dan siyasan wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya bayyana cewa sun yi magana da duk jami’an tsaro domin ganin yadda za a gano Dadiyata. Fiye da wata guda kenan abin ya ci tura.

Bayan haka kuma Abba Gida-Gida ya bayyana cewa daga lokacin da wannan abu ya faru zuwa yanzu, su na tare da Iyalin wannan Matashi mai ra’ayin siyasar Kwankwasiyya a Garin Kaduna.

KU KARANTA: APC ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa 'Dan Majalisar ta a Kano

Bugu da kari wannan ne ya sa Abba Yusuf ya aika Tawaga ta musamman a karkashin Darektan yakin neman zabensa, Yunus Dangwani, su ka tabbatarwa Iyayen Matashin kokarin da su ke yi.

Ganin duk an yi wannan, Injiniya Kabir Yusuf ya na ganin lokaci ya yi, inda ya ce ya na kira ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro su maida hankalinsu wajen gano Dadiyata su kubutar da shi.

A cikin makon nan ne shugaban ‘Darikar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, ya fito shafinsa na Tuwita shi ma ya na kira ga jami’an tsaro su gano inda aka boye wannan Masoyin na su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel