APC ta jaddada dakatarwar da tayi wa Jibrin yayinda kotu ke shirin yanke hukunci kan zabensa

APC ta jaddada dakatarwar da tayi wa Jibrin yayinda kotu ke shirin yanke hukunci kan zabensa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Kano, ta jaddada dakatarwar da tayi wa Abdulmumin Jibrin, dan majalisa mai wakiltan mazabar Bebeji/Kiru a majalisar Tarayya.

Jam'iyyar reshen karamar hukumar Bebeji a baya ta dakatar da dan majalisan har na tsawon shekara daya bisa zargin daukakgudanar da ayyukan da suka saba ma jam’iyyar.

Suleiman Gwarmai, shugaban APC a Bebeji, yace hukucin dakatar da dan takaran ya zo ne, bayan kwamitin mutum bakwai da aka kafa domin bincikarsa ta bayar da shawarar yin haka bayan jam’iyyar ta karbi kara akan dan majalisan.

Jam'iyyar har ila yau ta kafa kwamiti don duba ga lamarin zargin da aka yi ma Jibrin.

Amman a ranar Laraba, Ibrahim Sarina, Sakataren jam’iyya mai mulki a jihar, yace bayan karanta rahoton da aka gabatar, kwamitin ta karfafa dakatarwan.

Hakan ya zo ne a wani wasika mai dauke da kwanan wata 4 ga watan Satumba, jaridar TheCable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Dasuki ya sha kaye a kotun zaben jihar Sokoto

Lamarin ya zo ne gabannin lokacin da kotun zabe ke kokarin yanke hukunci akan zaben mazabarsa.

Ko da yake hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe, abokin takarar nasa ya ya kalubalanci nasaran shi a kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel