Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 2 a wasu hare hare da suka kai a Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 2 a wasu hare hare da suka kai a Borno

Akalla mutane biyu ne suka gamu da ajalinsu sakamakon wani hari da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka kai yankin Nganzai na jahar Borno, inda suka kona gidajen jama’a da dama, inji rahoton Sahara Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan ta’addan sun kaddamar da harin ne a garin Gajiram, babban garin karamar hukumar Nganzai da misalin karfe 5 na yammcin Laraba, 4 ga watan Satumba, inda har suka kona ofishin DPO na Yansanda da kuma karfen sabis na wata kamfanin sadarwa.

KU KARANTA: Mun cire shingayen jami’an tsaro a kan hanyar Abuja da Birnin Gwari – El-Rufai

Wani matashi dan sa kai ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace jama’an garin da dama sun tsere zuwa cikin daji domin tsira da ransa daga maharan, yayin da yan bindigan suka kwashe duk wani kayan abinci da suka yi ido hudu da shi.

Wannan shi ne karo na uku da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suke kai ma garin Gajiram hari, ba tare da sun samu wani tirjiya daga dakarun rundunar Sojan Najeriya ba.

A wani labarin kuma, dakarun rundunar Operation Lafiya Dole dake garin Maiduguri sun kama wasu manyan motoci guda hudu tare da direbobinsu da suke dakon kayayyakin abinci da zasu kai ma mayakan ta’addanci na Boko Haram a cikin daji.

Sojojin suna zargin su kansu direbobin motocin yan Boko Haram ne sakamakon hukumar Soja ta haramta sayar ma kungiyar kayan abinci, man fetir da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

Kwamandan yaki da ta’addanci, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ne ya bayyana haka yayin da yake jagorantar aikin lalata kayayyakin tare da konasu a garin Maiduguri, inda yace hukumar Soji ta haramta sayar ma Boko Haram duk wasu kayan da take bukata ne don rage mata karsashi tare da dakile ayyukanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel