Yanzu-yanzu: Kasar Afrika ta kudu ta kulle ofishohin jakadancinta dake Abuja da Legas

Yanzu-yanzu: Kasar Afrika ta kudu ta kulle ofishohin jakadancinta dake Abuja da Legas

- Hare-haren ramuwar gayya da yan Najeriya ke kaiwa kasuwannin yan kasar Afrika ta kudu ya tursasa gwamnatin kasar kulle ofishin jakadancinta dake Najeriya

- Jakadan Afrika ta kudu zuwa Najeriya ya kulle ofishohin jakadancin kasar dake Legas da Abuja

- Jakada Moroe, ya ce za'a bude ofishohin inda an kwatar da kura

Jakadan kasar Afrika ta kudu ya kulle ofishin jadakancin kasar dake Legas da Abuja kan ramuwar gayyan da yan Najeriya ke yi.

The Nation ta bada rahoton cewa mukaddashin jakadan kasar Afrika ta kudu, Ambasada Bobby Moreo, ya bada umurnin dakatad da duk wani harkar demokradiyya har sai kurar ta kwanta.

Legit.ng ta kawo muku rahotannin yadda yan Najeriya a jihohi daban-daban suke kai hare-hare kasuwannin yan kasar Afrika ta kudu domin nuna bacin ransu kan yadda ake kashe yan Najeriya a kasar Afrika ta kudu.

KU KARANTA: Tsohuwa mai shekaru 74 za ta haifa tagwaye bayan shekaru 54 da aure

A cewar Moreo, dalilin da ya tursasa kulle ofishoshin jakadancin shine hare-haren da yan Najeriya ke kaiwa.

Yace: "An umurceni na kulle ofishohin jakadancinmu har sai an kwantar da kuran. Mun samu labarin cewa ana kaiwa yan kasar Afrika ta kudu hari."

A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, 4 ga watan Satumba, ya sammaci jakadan Najeriya dake kasar Afrika ta kudu ya dawo gida.

Hakazalika ya ce Najeriya ta fasa halartan taron tattalin arzikin duniya da za'ayi a makon nan a kasar Afrika ta kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel