Ta kwana gidan sauki: Najeriya za ta fara sayar da tikitin shiga jirgin kasa a yanar gizo

Ta kwana gidan sauki: Najeriya za ta fara sayar da tikitin shiga jirgin kasa a yanar gizo

Shirye shirye sun yi nisa don fara sayar da tikitin shiga jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja a shafukan yanar gizo don kauce ma badakalar da ake samu a tashoshin jirgin, wanda hakan ke janyo rikici tsakanin matafiya da jami’an hukumar.

Jaridar Leadership ta ruiwato hukumar da hakkin tsara cinikin yanar gizo a Najeriya ya rataya a wuyarta, watau, Infrastructure Concession Regulatory Commission, ICRC, ce ta bayyana haka yayin ta bakin shugabanta, Chidi Izuwah yayin da yake mika takardun kasuwancin ga ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

KU KARANTA: Mun cire shingayen jami’an tsaro a kan hanyar Abuja da Birnin Gwari – El-Rufai

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana cewa: “Ka yi alkawarin samar da mafita ga yamutsin da ake samu a tashoshin jiragen kasa, don haka a yau muka kawo maka cikakken takardar kasuwancin sayen tikiti ta yanar gizo.

“Wannan tsarin na tsawon shekaru 10 ne, kuma a shekaru goman nan gwamnatin tarayya da hukumar jirgin kasan Najeriya za su samu naira biliyan 16 a matsayin kudaden shiga, amma wannan tsarin hadin gwiwa ne tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

“Kamfanonin za su zuba hannun jari don samar da manhajar da matafiya zasu iya sayen tikitin cikin sauki a yanar gizo kamar yadda ake yi a duk fadin duniya, kuma a yanzu haka hukumar NRC ta zabo kamfanin SECURE ID a matsayin wanda za su shiga wannan hadaka da ita.

“Wannan tsarin zai kara samar da kudaden shiga ga gwamnati, zai kawar da cin hanci da rashawa, sa’annan zai baiwa matafiya daman zaban farashin kujerar da suke so.” Inji shi.

Daga karshe minista Amaechi ya bayyana farin cikinsa da wannan takarda, haka zalika ya gode ma shugaban ICRC bisa kokarin da ya yi wajen kammala wannan aiki cikin kankanin lokaci, sa’annan ta tabbatar masa da cewa zai mika batun ga majalisar zartarwa domin samun amincewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel