Xenophobia: An haramta wa direbobin Afrika ta Kudu ketara iyaka zuwa kasashen Zimbabwe, Zambia da sauransu

Xenophobia: An haramta wa direbobin Afrika ta Kudu ketara iyaka zuwa kasashen Zimbabwe, Zambia da sauransu

Direbobin manyan motoci daga kasashen Afrika sun yi gargadin cewa ba za a bari direbobi daga kasashen Affrika ta Kudu su ketare iyakokinsu ba.

Direbobin wadanda suka kare hanyar wasu direbobin manyan motocin Afrika ta Kudu daga ketare iyakarsu, sunce wannan hanya ne na ramuwar gayya akan hare-haren da ake yiwa sauran yan kasashen Afrika a kasar Afrika ta Kudu.

A wani bidiyo da yayi fice a shafukan zumunta, direboin sunce ba za a bari direbobin manyan motoci na kasar Afrika ta Kudu su ketare iyakokin kasashen Zimababwe, Zambia, Bostwana, Namibia, Malawi, Tanzania, Mozambique da Congo ba.

Koda dai ba a gane a wacce iyaka bane aka dauki bidiyon, mutanen sunce daga yanzu sai dai direbobin Afrika ta Kudu su ajiye motocinsu a iyakar ko kuma su dauko hayar direban da ba dan kasarsu ba ya tuka motocin zuwa kasahensu.

Daya daga cikin mazajen a cikin bidiyon ya bukaci direban kasar Afrika ta Kudu wanda ya nadi bidiyon lamarin da ya je ya isar da sakon ga mutanensa.

KU KARANTA KUMA: Katsina: Yan bindiga sun gabatar da babban bukata da suke so a cika masu kafin su ajiye makamansu

A halin da ake ciki, mun ji cewa wani bidiyo da yake ta yawo a kafafen sadarwa, ya nuna yadda wani mutumi dan kasar Afrika ta Kudu ya bayyana ainahin abinda ya jawo wannan rikicin da yasa suke kashe baki a kasar su.

A cewar mutumin dan kasar Afrika ta Kudun, rikicin ya samo asali ne a lokacin da wani mutumi dan kasar Tanzaniya ya harbi wani direban motar haya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel