Gaskiyar abinda yasa 'yan Afrika ta Kudu suke kashe 'yan Najeriya

Gaskiyar abinda yasa 'yan Afrika ta Kudu suke kashe 'yan Najeriya

- Wani mutumi dan kasar Afrika ta Kudu ya bayyana ainahin dalilin da ya jawo rikici a kasar ta Afrika ta Kudu

- Mutumin ya ce wani dan kasar Tanzaniya ne ya kashe wani direban motar haya, shine abinda ya jawo wannan rikici tun fil azal

- Ya ce babu ruwan 'yan Najeriya a cikin wannan lamarin, saboda dama 'yan kasar Tanzaniya ne suke da matsalar safarar miyagun kwayoyi da kuma fashi da makami

A wani bidiyo da yake ta yawo a kafafen sadarwa, ya nuna yadda wani mutumi dan kasar Afrika ta Kudu ya bayyana ainahin abinda ya jawo wannan rikicin da yasa suke kashe baki a kasar su.

A cewar mutumin dan kasar Afrika ta Kudun, rikicin ya samo asali ne a lokacin da wani mutumi dan kasar Tanzaniya ya harbi wani direban motar haya.

Legit.ng ta ruwaito muku yadda lamarin ya samo asali, ma'ana lokacin da 'yan kasar Afrika ta Kudun suka fara kai wa bakin dake kasar hari, bayan kashe wani direban motar haya da wani mai safarar miyagun kwayoyi yayi a garin Pretoria ranar Talata.

KU KARANTA: Yadda Dino Melaye ya rushe da kuka, ya kuma fadi yaji ciwo bayan ya sha kasa a zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kogi

Mutumin dan kasar Afrika ta Kudun ya bayyana cewa mutumin mai safarar kwayoyin dan kasar Tanzaniya ne ba dan Najeriya bane.

'Yan kasar Tanzaniya sune aka sani da safarar miyagun kwayoyi da fashi da makami.

A wannan makon ne dai aka wayi gari 'yan kasar Afrika ta Kudu sun tashi suna bin duka bakin dake kasar su suna kashewa suna kone shaguna da gidajensu, wannan dalilin yasa da yawa daga cikin mutanen da ba 'yan kasar ba suka baza cikin dazuka domin tsira da ransu.

Hakan ya jawo kace nace matuka a Najeriya inda har wasu suka fara daukar doka a hannunsu suna kone wasu wurare na 'yan kasar Afrika ta Kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel