Yadda Dino Melaye ya rushe da kuka, ya kuma fadi yaji ciwo bayan ya sha kasa a zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kogi

Yadda Dino Melaye ya rushe da kuka, ya kuma fadi yaji ciwo bayan ya sha kasa a zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kogi

- Bayan an bayyana cewa ya sha kasa a zaben fidda gwani Sanata Dino Melaye ya rikice

- Inda ya dinga rusa ihu yana cewa an cuce shi ne a zaben da aka yi, sanadiyyar hakan ta sa yaji ciwo a guiwarsa

- A lokacin aka garzaya da shi zuwa asibiti domin yi masa magani a wajen ciwon da yaji

Kokarin da Dino Melaye yake yi na ganin ya zama gwamnan jihar Kogi ya zo karshe, bayan ya sha kasa warwas a wajen Injiniya Musa Wada, a lokacin zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP wanda aka yi a jiya Laraba.

Sanatan da yake da abubuwan ban dariya an hango shi lokacin da ya rushe da kuka yana ihu yana cewa an cuce shi ne a zaben.

Sanatan kuma yaji ciwo a guiwarsa sanadiyyar rikicin da ya barke a lokacin zaben fidda gwanin. Musa Wada kani ne ga tsohon gwamnan jihar Idris Wada.

KU KARANTA: Tashin hankali: Abinda zai faru da ace lokacin Abacha ne ake kashe mutane a kasar Afrika ta Kudu - Skiibii

A lokacin da lamarin ya faru dai aka yi gaggawar garzaya da Sanatan zuwa asibiti mafi kusa domin yi masa magani a ciwon da yaji din.

A jiya ne Sanatan ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari akan maganar da yayi dangane da kisan mutane da ake yi a kasar Afrika ta Kudu.

Sanatan ya caccaki shugaban kasar inda ya nemi da ya jagoranci tawagar da ya tura kasar Afrika ta Kudun tunda shima ya taba zama Janar na soja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel