Enugu: TUC za ta tafi yajin aiki idan aka ki dabbaka karin albashi

Enugu: TUC za ta tafi yajin aiki idan aka ki dabbaka karin albashi

Shugaban kungiyar TUC ta ‘yan kasuwa na reshen jihar Enugu, ya yi gargadi cewa idan har tattaunawar da ake yi game da karin albashi ya bi ruwa, za su dauki matakin da ya dace.

Chukwuma Igbokwe ya nuna cewa muddin zaman da ake yi na tsara yadda za a karawa ma’aikata albashi bai kai ga ko ina ba a wannan karo, babu abin da zai hana su daukar matakin yin yaji.

Igbokwe ya yi wannan jan-kunne ne a lokacin da ya zanta da Manema labarai a Ranar Laraba, 4 ga Watan Satumban 2019 domin yi wa Duniya bayanin yadda tattaunawar ta ke ciki a Abuja.

“Abin da kurum ya rage mana shi ne mu dauki mataki. Idan aka gaza samun matsaya a zaman wannan karo, shugabannin mu da ke birnin tarayya za su kira taron zartarwa.” Inji Igbokwe.

KU KARANTA: Za a fitar da kasafin kudin shekarar 2020 kwanan nan

A cewar shugaban wannan kungiya ta Enugu: “Idan mu ka zauna, za mu duba abubuwan da mu ke da su, sai mu dauki matakin da zai yi aiki a kaf fadin kasar nan.” A nan ne za a dauki duk wani mataki.

Mista Igbokwe ya na sa ran cewa abubuwa za su tafi daidai ganin cewa shugaban ma’aikatan kasar, Wilfried Eyo Ita, ta dawo aiki don haka za a yi maza a cin ma yadda za a fitar da karin albashin.

Jagoran ‘yan kwadagon ya nuna cewa abin da su ke nema wajen gwamnati ba mai yawa ba ne musamman ganin an sa hannu a dokan karin albashin, sai dai kurum a fara dabbaka wannan doka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel