Mawakiyar Najeriya Tiwa, da ‘Dan wasa BasketMouth sun kauracewa kasar SA

Mawakiyar Najeriya Tiwa, da ‘Dan wasa BasketMouth sun kauracewa kasar SA

Babbar Mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage, ta janye kanta daga wasan da ta shirya yi a kasar Afrika ta Kudu kwanan nan. Hakan na zuwa ne bayan harin da aka kai wa wasu baki a kasar.

An shirya tsaf cewa Tiwa Savage za ta yi wani wasa a wajen wani shararren biki da kamfanin DSTV ta shirya a kasar ta Afrika ta Kudu a Ranar Asabar, 21 ga Watan Satumban nan na 2019.

Yanzu Mawakiyar ta fasa zuwa wannan biki bayan samun rahoton ana aukawa shagon ‘Yan Najeriya ana kona masu dukiya, sannan ana kona motocin da ke dauke da ‘yan kasar waje.

Tiwa Savage a shafinta na Tuwita @tiwasavage, ta fito ta ce: “Ba zan bari in ta kallon ana yanka mutanena a kasar Afrika ta Kudu ba. Wannan rashin hankali ne.”

Mawakiyar ta cigaba da cewa: “A dalilin wannan, ba zan yi wasan 21 ga Watan Satumba na DSTV a babban birnin Johannesburg ba. Ina addu’a ga Iyalan wadanda wannan rashi ya auka masu.”

KU KARANTA: Dangote da Otedola sun yi magana game da rikicin Afrika ta Kudu

Jama’a da dama musamman a Najeriya, sun fito su na jinjinawa wannan matsaya da Mawakiyar ta dauka. Ko da dai wasu daga kasar Afrika ta Kudu sun caccaki ‘yar wasan a kan wannan.

A daidai wannan lokaci babban ‘dan wasan ban dariyar nan, Mista Bright Okpocha wanda jama’a su ka fi sani da Basketmouth, ya fasa shiga kasar Afrika ta Kudun saboda irin wannan dalili.

A shafinsa, Basketmouth ya ce: “Ban sa ya aka yi kuma yaushe mu ka samu kan mu a nan ba. Ba zan halarci bikin bada lambar yabon da aka shirya karshen makon nan a kasar Afrika ta Kudu ba.”

‘Dan wasan ya karasa da cewa: “Za a ji abin kamar rada. Amma idan har mu ka hadu mu ka hada kai, za a samu banbanci, sannan kuma za a ga canji. Amma a yau dai kam, kan mu ya na hade.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel