Kashe-kashe: Bukola Saraki, Aliko Dangote da Otedola sun nemi ‘Yan Afrika su hada kai

Kashe-kashe: Bukola Saraki, Aliko Dangote da Otedola sun nemi ‘Yan Afrika su hada kai

Mun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya fito yana mai Allah-wadai da wasu ‘Yan Najeriya da ke kai wa mutanen kasar Afrika ta Kudu harin ramuwar gayya.

Dr. Bukola Saraki ya yi magana ne a kan hare-haren da ake kai wa a dalilin farmakin da aka yi wa wasu daga cikin mutanen Najeriya da sauran kasashen Afrika da ke ci rani a kasar Afrika ta Kudu.

Bidiyoyin da ke nuna ‘Yan Najeriya su na kai harin ramuwa a Najeriyar a kan kasuwancin wasu da ake yawon kuskuren dauka cewa mutanen kasar Afrika ta Kudu ne abin takaici ne da tada hankali.”

A shafin na sa. tsohon Sanata da kuma gwamnan na jihar Kwara ya cigaba da cewa: “A matsayin mu na mutane, bai kamata mu bari mu zame mu fadawa dabi’ar rashin sanin darajar ‘Dan-Adam ba.”

KU KARANTA: Tsohuwar Ministar Najeriya ta na halartar taron da aka yi a Afrika ta Kudu

Bai kamata mu burma cikin abin da mu ke Allah-wadai da shi ba. Ina kira ga ‘Yan Najeriya su nuna dattaku, su kuma sa hakuri a daidai wannan lokaci. Dole mu yi tir da wannan ta’adi da hare-hare.

Saraki duk ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Tuwita jiya, Laraba, 4 ga Watan Satumba, 2019 da kusan karfe 11:00 na safe a agogon Najeriya, yayin da alamu ke nuna cewa shi ya na Birnin Landan.

A farkon makon nan da wannan rikici ya fara, Saraki, ya nuna takaicinsa inda ya yi kira a kyale mutanen Najeriya su cigaba da neman abincinsu a kasar wajen tare da kira ga shugabanni su zauna.

#XenophobicAttacks #NoToHate #NoToDestruction

KU KARANTA:

Hamshakin Attajirin nan, Aliko Dangote da Femi Otedola su ma sun yi Allah-wadai da harin gayyar da ‘Yan Najeriya su ka koma kai wa. Dangote ya nemi mutanen Afrika su ajiye kiyayya gefe.

Femi Otedola ya yi jimamin abin da ya ke faruwa a Kudancin Afrikar inda ake hallaka mutanen Najeriya babu dalili. Otedola ya nemi jama’a su hada kai su yaki wannan kashe-kashe da ake yi a Nahiyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel