WEF: Oby Ezekwesili da Jim Ovia sun halarci taron da ake yi a Afrika ta Kudu

WEF: Oby Ezekwesili da Jim Ovia sun halarci taron da ake yi a Afrika ta Kudu

Tsohuwar Ministar Najeriya, Misis Oby Ezekwesili, da shugaban bankin Zenith, Jim Ovia, sun jawo abin magana bayan da su ka halarci taron tattalin arzikin da ake yi a kasar Afrika ta Kudu.

Wadannan manyan mutane sun halarci taron ne a daidai lokacin da kasashen Afrika su ke kwayewa Afrika ta Kudu baya a dalilin harin da mutanenta su ka kai wa ‘Yan Najeriya da wasu.

Rikicin da ake yi ya sa gwamnatocin kasashe har da Najeriya su ka janye daga wannan taro na WEF da aka shirya a Kudancin Afrikan. Duk da wannan Ezekwisili da Ovia ba su fasa halarta ba.

Oby Ezekwisili da Mista Jim Ovia su na cikin wadanda su ka jagoranci wani zama da aka yi wajen wannan taro na Duniya jiya. A da, an shirya cewa shugabannin Najeriya za su halarci zaman..

Wannan ya sa jama’a su ka dura kansu a shafin Tuwita inda mutane su ke ta kiran musamman #MadamOby wanda ta nemi takarar shugaban kasa a zaben bana na 2019 amma ta sha kashi.

KU KARANTA: An fara kira ga ‘Yan Najeriya da ke kasar Afrika ta Kudu su dawo kasarsu

Kate Nnaji ta fito shafin Tuwita ta na cewa: “Da ace mun zabi Madam Oby a matsayin mace shugabar kasa ta farko, da haka za ta tattara ta tafi kasar Afrika ta Kudu duk da abin da ke faruwa?”

Olufunke Lawson kuwa cewa ya ke yi: “Madam Oby ta tafi taron WEF ne domin ta samu ‘yan daloli, sannan ta tsayawa ‘Yan Najeriya da aka ci mutuncin su kenan ko mene? Kash! Tir!”

Ita kuwa Favour Onyeoziri ta na ganin: “Madam Oby ta zabi ta je kasar Afrika ta Kudu ta yi magana kan harin da ake kai wa baki, bayan gwamnati ta san da wannan sarai, amma ta yi mursisi. Rashin zuwanta da ya fi zuwa amfani.”

Shi ma Jim Ovia ba a barsa a baya ba inda mutane da-dama su ka fito shafin na Tuwita su na sukarsa. Wasu kuma su na ganin halartar manyan zai bada a kawo karshen wannan rikici.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel