Afirka ta Kudu: Jiragen Air Peace za su kwaso ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu zuwa gida, inji Onyeama

Afirka ta Kudu: Jiragen Air Peace za su kwaso ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu zuwa gida, inji Onyeama

Ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya ta sanar da al’ummar kasar cewa jiragen Air Peace za su debo ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudun zuwa gida Najeriya saboda kisan gillan da ake yi masu a can kasar.

Mai kamfanin jiragen Air Peace Cif Allen Onyema ya dauki nauyin tura jiragensa domin yin wannan aiki na dawo da ‘yan Najeriya gida kyauta.

KU KARANTA:Kafin karshen watan Satumba zamu fitar da kasafin kudin 2020 – Zainab Ahmed

A don haka ma’aikatar na kira ga al’ummar Najeriya cewa duk wanda yake da danuwa a kasar Afirka ta kudu ya sanar da shi labarin wannan garabasar domin ka da ta wucesa.

Kamar yadda shugaban kamfanin Air Peace ya bayar da sanarwa jiragen za su bar Najeriya ne zuwa kasar Afirka ta Kudu a ranar Juma’a 6 ga watan Satumba domin kwaso ‘yan Najeriya mazauna kasar.

Rahotanni daga jaridar Vanguard sun bayyana mana cewa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya, Mista Ferdinand Nwonye ne ya fitar da wannan sanarwa kunshe a cikin wani zance da ya samu sa hannunsa.

Ga abinda zance nasa ya fadi: “Ana kira ga dukkanin ‘yan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu da su tuntubi ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Johannesburg domin samun karin bayani game da yadda wannan shirin zai kasance.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel